Home Labaru Takaddama: Lauyan Kare Hakkin Bil Adama Ya Maka Gwamnatin Tarayya Kotu

Takaddama: Lauyan Kare Hakkin Bil Adama Ya Maka Gwamnatin Tarayya Kotu

302
0

Wani Lauya mai kare hakkin bil-Adama Malcomn Omirhobo, ya shigar da gwamnatin Nijeriya kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin a dakatar da ita daga ba kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Naira biliyan 100.

Omirhobo, wanda shi ne jagoran shigar da karar a karkashin gidauniyar sa, ya nemi kotu ta hana gwamnatin tarayya bada kudaden kamar yadda ministan cikin gida ya yi wa kungiyar alkawari.

A cikin karar da lauyan ya shigar, ya ce wadannan kudade ne masu yawan gaske, wanda za a iya amfani da su wajen yin muhimman ayyukan more rayuwa, kuma za a iya bada kudin har ila yau domin taimakon masu kananan sana’o’i.

Karar da lauyan ya shigar dai ta shafi gwamantin Nijeriya, da ministan shari’a, da ministan cikin gida, da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, da kuma ma’ajin gwamnatin tarayya.

Bugu da kari, lauyan ya sake gabatar da kara a kan yunkurin da Shugaba Buhari ke yi na dakatar da lasisin mallakar bindiga, inda ya ce shugaban kasa ba ya da wannan iko, domin ana rike bindiga ne saboda kare kai.

Leave a Reply