Home Labaru Kiwon Lafiya Takaddama: Kungiyar Yaki Da Yunwa Ta Dakatar Da Aiki A Jihar Borno

Takaddama: Kungiyar Yaki Da Yunwa Ta Dakatar Da Aiki A Jihar Borno

485
0

Kungiyar bayar da tallafi ta Action Against Hunger ta ce matakin da sojin Nijeriya ta dauka na rufe ofisoshinta, ba tare da sanarwa ko bayani ba ne suka sa ta dakatar da aikin ba da tallafi ga miliyoyin ‘yan Najeriya a yankin arewa masu gabas.

Rundunar sojojin Najeriya karkashin Operation Lafiya Dole dai, ta ayyana kungiyar a matsayin wadda ba a maraba da ita a Najeriya, saboda abinda ta kira taimakawa ‘yan  Boko Haram da na kungiyar ISWAP.

Sanarwar da mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Ado Isa, ya wallafa a shafin sada zumunta na cewa a karo da dama sojoji sun ankaras, game da irin wadannan aikace-aikace da ba su dace ba.

Rundunar ta ce suna taimaka wa ‘yan Boko Haram  ne ta hanyar kai musu agajin abinci da magunguna duk da gargadin da rundunar ta sha yi musu.

Sai dai kungiyar Action Against Hunger ta ce ta na gudanar da aikin jin ‘kai ne ga  dan’adam a matsayinta na kungiya mai cin gashin kai, ta ce su ‘yan ba-ruwan sune.

Sannan kuma ba sa nuna fifiko ga miliyoyin al’ummar jihar Borno ta hanyar samar da muhimman ayyuka ga mutane mafi rauni, musamman mata da kananan yara.

Leave a Reply