Home Labaru Takaddama: Kotu Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci A Kan Takardun...

Takaddama: Kotu Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci A Kan Takardun Karatun Buhari

387
0

Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta ce nan gaba kadan za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar game da sahihancin takardar shaidar kammala karatun sakandare na Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya yi amfani da ita wajen shiga takarar zaben shekara ta 2019.

Bayan ta saurari bayanai daga masu shigar da kara da bangaren wadanda ake kara, Kotun ta ce za ta bayyana masu ranar da za a yanke hukunci da zarar ta kammala nazari.

Yayin zaman kotun a ranar Litinin da ta gabata, lauyan masu shigar da kara Ukpai Ukairo ya dage a kan cewa, shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takara ba idan aka yi la’akari da takardun shaidar zurfin ilmin sa.

Lauyan ya cigaba da cewa, shugaba Buhari bai hada da takardar shaidar kammala karatun sakandare a takardun da ya cike na neman tsayawa takara da hukumar zabe ta tanada ba.

A karshe ya roki kotu ta yanke hukunci ta hanyar wancakalar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce shugaba Buhari ya cancaci tsayawa takara.

Leave a Reply