Home Labaru Takaddama: Kotu Ta Tsare Ɗan Kasuwa Bisa Zargin Zagin Fintiri A Shafin...

Takaddama: Kotu Ta Tsare Ɗan Kasuwa Bisa Zargin Zagin Fintiri A Shafin Facebook

44
0
Facebook

Wata Kotu ta bukaci a cigaba da tsare wani ɗan kasuwa mai Ali Numan bisa zargin shi da zagin gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

Mai shari’a Japhet Ibrahim Basani na wata kotun majistare, ya umarci a cigaba da riƙe Ali Numan da ake tuhuma da zagin gwamna Fintiri a shafin sada zumunta.

Wata majiya ta ce, an samu Numan da laifin sukar gwamnan cikin harshen Hausa da Fulanci a shafin sa Facebook, inda ya bayyana Fintiri a maysayin barayo kuma jagoran ɓarayin Nijeriya.

Haka kuma, an zargi Numan da iƙirarin cewa, gwamnan ya saci taliya da daruruwan bilyoyin naira.

A cewar masu shigar da kara, kalaman da Numan ya yi amfani da su kokari ne na tada zaune tsaye tsakanin magoya bayan gwamnan.

Tuni dai an ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Agusta na shekara ta 2021.