Home Labaru Takaddama: Kotu Ta Hana Hukumar Zabe Ta Ba Okorocha Shahadar Lashe Zabe

Takaddama: Kotu Ta Hana Hukumar Zabe Ta Ba Okorocha Shahadar Lashe Zabe

251
0
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Owerri na jihar Imo, ya dakatar da hukumar zabe kasa daga mika wa Rochas Okorocha shahadar lashe zaben kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Imo ta Yamma.

Rochas Okorocha dai na ci-gaba da fuskantar matsaloli, tun bayan zaben Watan Fubrairu na shekara ta 2019, inda mai shari’a E.F. Njemanze ya nemi hukumar zabe ta ajiye maganar ba Okorocha shahadar lashe zaben nasara tukunna.

Kotun ta shaida wa hukumar zabe ta koma kan matsayar ta, bayan ta fara tunanin yin amai ta lashe ta hanyar ba Rochas takardar da ke nuna cewa ya lashe zaben.

Abokin karawar Rochas Okorocha, Jones Onyeriri ne ya kai kara a gaban kotun, ya na kalubalantar nasarar da Rochas ya samu a zaben shekara ta 2019 na ‘dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar yankin Imo ta Yamma.

Yanzu haka dai, kotun ta bukaci hukumar zabe ta jinge maganar ba Okorocha shahadar har sai zuwa lokacin da aka kammala sauraren karar da ake yi, yayin da alkalin kotun ya dage zaman sauraren shari’ar zuwa ranar Laraba 5 ga Watan Yuni na shekara ta 2019.