Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG Christopher Galtier ya bayar da tabbacin cewa Lionel Messi zai raba gari da kungiyar bayan doka wasan karshe tsakanin kungiyar da Clermont a gobe asabar.
Kalaman na Galtier na zuwa ne bayan jita-jitar da ta baza gari kan yiwuwar tafiyar Messi mai shekaru 35 a karshen wannan kaka wato bayan karewar kwantiragin sa.
A watan Yulin 2021 ne Messi ya koma PSG da taka leda bayan karewar kwantiragin sa da Barcelona, kungiyar da ya fara taka leda da ita tun ya na karamin yaro, inda bayan zuwan sa Paris ya taimaka wajen dagawa kungiyar kofunan Lig 12.
A jawabinsa kan rabuwar PSG da Messi, Galtier ya ce abin alfahari ne gareshi samun damar horar da dan wasan mafi daraja da duniya ta taba gani.
Galtier ya ce wasan na gobe zai zama karo na karshe da za a ga kafar Messi a Parc des Prince ya na wakiltar PSG, inda za ayi masa wata girmamawar bankwana bayan kammala wasan na gobe.
Tafiyar ta Messi na zuwa ne bayan takaddamar da ta shiga tsakanin sa da PSG sakamakon balaguron da ya yi zuwa Saudi Arabia ba tare da masaniyar kungiyar ba, gabanin dan wasan na Argentina ya nemi afuwa.