Home Labaru Takaddama: Gwamnatin Zamfara Ta Ba Matawalle Wa’Adin Maido Da Motocin Alfarma Na...

Takaddama: Gwamnatin Zamfara Ta Ba Matawalle Wa’Adin Maido Da Motocin Alfarma Na Biliyoyin Naira

95
0

Gwamnatin jihar Zamfara ta ba tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa’adin kwana biyar ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin naira da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ɓatar-dabo.

A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai Sulaiman Bala Idris ya fitar ya ce sabuwar gwamnati ta samu hujja da alaƙaluman kuɗin da aka ware wajen sayo wasu manyan motocin alfarma.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta samu hajja mai ƙarfi da ke nuna cewa tsohon gwamnan ya ware biliyoyin naira wajen sayo manyan motocin alfarma da gwamnati za ta yi amfani da su.

Sai dai sanarwar ta ce sabuwar gwamnati ba ta samu ko da mota guda cikin motocin da tsohuwar gwamnatin ta ce ta sayo, kamar yadda bayanai suka nuna ba.

A baya-bayan nan dai tsohon gwamnan na jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle na ta samun taƙun-saka da hukumar yaki da cin hanci da rasha EFCC bayan da ya zargi shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa, da aikata almundahana iri-iri.

Leave a Reply