Home Labarai Takaddama: Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Murabus Din Babban Limamin  Masallacin Wala

Takaddama: Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Murabus Din Babban Limamin  Masallacin Wala

36
0

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta Jihar Kebbi, ta amince da
murabus din babban limamin masallacin juma’a da ke Wala a
Birnin Kebbi, Sheikh Rufa’i Ibrahim Bashar.


Ma’aikatar ta kuma amince da nadin mataimakin limamin masallacin, Malam Mammam Nata’ala Yahaya, domin ya zama Limamin Masallacin a matsayin mai riko.


Kwamishinan ma’aikatar, Muhammad Sani Aliyu, ya bukaci Majalisar Masarautar Gwandu da ta nada babban Limamin
Masallacin Wala na Juma’a.


Kwamishinan ya karyata rade-radin da ake cewa Sheikh Rufa’i Ibrahim Bashar ya bar matsayinsa kan batun kudi.


 Gwamna Nasir Idris ya bayar da tallafin kudi ga limaman masallatan juma’a na jihar domin taimaka musu wajen rage wahalhalun da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki a halin yanzu da kuma taimakon na kusa da su.

Leave a Reply