Home Labaru Takaddama: Dattawan Kano Sun Gargadi Buhari Da Ganduje Kan Sabbin Masarautu

Takaddama: Dattawan Kano Sun Gargadi Buhari Da Ganduje Kan Sabbin Masarautu

640
0

Wasu dattawaa jihar Kano, sun gargadigwamnaUmar Ganduje a kan matakin da ya dauka na nada sabbin sarakuna 4 masu daraja ta daya, lamarin da su ka ce zai iya haifar da rikici.

Dakta Abubakar Sadiq Muhammad da Bashir Yusuf Ibrahim da Bashir Tofa da Dakta Usman Bugaje da kuma Farfesa Jibril Ibrahim, su na daya daga cikin wadanda suka gargadi Ganduje a cikin wata sanarwa da suka fitar.

Sanarwar, ta kuma bukaci shugabaMuhammdu Buhari ya sa baki a maganar, domin tsawatawa Ganduje ya janye matakin da ya dauka.

Gargadin dattawan dai ya na zuwa ne, bayan Babbar kotun Jihar Kano ta soke nadin sabbin sarakunan da Ganduje ya nada, sannan kotun ta bayyana matakin a matsayin abin da ya saba wa doka, tare da bukatar a koma a kan tsarin da ake kai kafin ta kammala sauraren karar da aka shigar a gabanta.

Masu Zaben Sarki a masarautar Kano da suka hada da Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Abubakar, da Sarkin Bai Alhaji Mukhtar Adnan, da Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani, da Makaman Kano Alhaji Sarki Ibrahim Makama ne suka garzaya kotu don kalubalantar matakin Ganduje na kirkirar sabbin masarautun hudu.