Babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara ta fuskar watsa labarai Ismail Misilli, ya musanta zargin cewa su na yi wa tsohon gwamnan jihar bi-ta-da-kulli a kan saida kayan gwamnati na miliyoyin Naira.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Isma’il ya ce ya zama dole a shaida wa duniya cewa gwamna Inuwa Yahaya mutane ne su ka zabe shi a kananan hukumomi 11 da ke fadin jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta rasa gane dalilin da ya sa ake tunanin ana yi wa tsohon gwamnan jihar bi-ta-da-kulli, duk da cewa binciken ‘yan kwamitin kwato kadarorin jihar ya tabbatar da cewa, akwai hannun tsohon gwamnan a cikin saida kadarorin jihar
Isma’il ya kara da cewa, kwamitin kwato kadarorin jihar a karkashin jagorancin Peter Bilal, an dora ma shi alhakin gano yadda aka yi gwanjon kadarorin jihar a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo, wanda hakan ya sa dole akwai muhimman tambayoyi da za a yi.