Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta bayyana kwararan dalilan ta na amfani da bidiyon ministan sadarwa Ali Isa Pantami, domin kwatanta wa ‘yan Nijeriya abubuwan da ke faruwa na matsalolin rashin tsaro a Nijeriya.
A’isha Buhari dai ta wallafa bidiyon ministan, wanda ke nuna ya na wa’azi dangane da kashe-kashen da ake yi a lokacin mulkin Goodluck Jonathan, inda ya ce shi Ubangiji kadai ya ke tsoro ba wani mutum ba.
Kamar yadda ta yi tsokaci kan bidiyon, A’isha Buhari wallafa cewa a cire tsoro a yi abin da ya kamata, lmarin da ya janyo cece-kuce har wasu na cewa ta na bayyana gazawar mulkin mai gidan ta kamar yadda ta dade ta na yi a tsawon shekaru
Bayan surutai sun yawaita ne A’isha Buhari ta kara yin wata wallafar, inda ta ce ta yi amfani da bidiyon ne don ta bayyana yadda yin abin da ya dace ba tare da tsoro ba ya ke haifar da da mai ido.