Home Labaru Takaddama: Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Umurnin Bude Tashoshin Ait Da Ray...

Takaddama: Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Umurnin Bude Tashoshin Ait Da Ray Power

344
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi umurnin sake bude tashoshin yada labarai na gidan talabijin na AIT da na rediyon Ray Power.

Da ya ke yanke hukunci, mai shari’a Ekwo Inyang ya umurci bangarorin su cigaba da kasancewa yadda su ke a ranar Juma’ar nan.

Mai shari’a Ekwo, ya kuma bukaci bangarorin su bayyana a gaban kotu ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni domin sauraren shari’ar.

A ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ne, hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Kasa NBC, ta janye lasisin yada labarai na Kamfanin sadarwa na Daar Communications Ltd.

Kamfanin Daar Communications, mallakar Raymond Dokpesi, su ke da gidan talbijin na AIT da Gidan Radiyon Ray Power a fadin Nijeriya.

Babban Daraktan hukumar NBC Modibbo Kawu ne ya sanar da manema labarai matakin dakatarwar a Abuja.

Leave a Reply