Home Home Takaddama: Ana Musayar Kalamai Tsakanin Bangaren Atiku Da Tinubu

Takaddama: Ana Musayar Kalamai Tsakanin Bangaren Atiku Da Tinubu

220
0
Wata takaddama ta kaure tsakanin bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da bangaren jigo a Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu dangane da zaben shugaban kasa na 2007 lokacin da Atiku ya yiwa Jam’iyyar AC takara.

Wata takaddama ta kaure tsakanin bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da bangaren jigo a Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu dangane da zaben shugaban kasa na 2007 lokacin da Atiku ya yiwa Jam’iyyar AC takara.

Wannan ya biyo bayan ikrarin da tsohon gwamnan jihar Osun Bisi Akande ya yi ne, na cewar Atiku yaki fitar da kudin sa domin yakin neman zaben shugaban kasa lokacin da Jam’iyyar AC ta tsayar da shi takara, inda duk lokacin da aka bukaci kudin aiki sai ya ruga wurin Bola Tinubu.

Akande ya ce duk lokacin da jam’iyyar ta bukaci kudin da zata gudanar da aiki, sai Atiku ya cewa Bola Tinubu ya taimaka abinda ke nuna cewar Tinubu ne kadai yake kashewa jam’iyyar kudi, bayan ya sadaukar da kudaden sa wajen gina sabuwar jam’iyyar ta AC a wancan lokaci wadda ta baiwa tsohon mataimakin shugaban kasar takara.

Sai dai kakakin Atikun Paul Ibe ya shaida cewa wannan ba wani abin damuwa bane, domin kuwa a lokacin Tinubu da Atiku suna inuwar jam’iyyar guda ne, saboda haka duk wanda ya ba jam’iyyar kudi ya bayar ne domin cimma muradun ta.

Ibe ya kara da cewar abin takaici ne yadda Bisi Akande ya zama karen farautar Tinubu, domin kuwa Atiku a wancan lokacin ya kashe makudan kudade wajen tafiyar da jam’iyyar ta su ta AC domin kalubalantar PDP.

Kakakin Atikun yace matakin da Akande ya dauka na bayyana Tinubu a matsayin mutumin da yafi kashe kudaden sa domin tafiyar da jam’iyyar ya nuna cewar yana fama da matsalar mantuwa.

Leave a Reply