Home Labaru Takaddama: An Bayyana Wa Kotun Zabe Cewa Shugaba Buhari Ya Yi Jarrabawar...

Takaddama: An Bayyana Wa Kotun Zabe Cewa Shugaba Buhari Ya Yi Jarrabawar Waec

262
0

Babban jami’in hukumar WAEC Henry Adeuwumi ya tabbatar da cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya zana jarrabawar a shekara ta 1961, inda ya samu shaidar jami’ar Cambridge ya kuma ci kwasa-kwasai biyar.

Yayin da a ke ta faman tafka muhawara a game da takardun karatun shugaba Muhammadu Buhari, hukumar shirya jarabawar WAEC ta hallara a gaban kotun da ke sauraren karar zaben shugaban kasa na shekara ta 2019.

WAEC na shugaba Muhammadu Buhari

Adewumi ya bayyana haka ne, yayin da ya bayyana a gaban Alkalan da ke sauraren korafin zaben shugaban kasa na shekara ta 2019.

A Ranar Talatar nan ne, shugaba Muhammadu Buhari ya fara kare kan sa a gaban kotu, inda ya ke kokarin gamsar da kotu cewa lallai shi ne ainihin wanda ya lashe zaben shekara ta 2019.

Shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari ya bayyana a gaban kotun, inda ya sanar da ita cewa Buhari ya na da takardar jarabawar WAEC.