Home Labaru Taimakawa Gwamnatin: NOA Ta Nemi ‘Yan Najeriya Su Ba Da Hadin Kai...

Taimakawa Gwamnatin: NOA Ta Nemi ‘Yan Najeriya Su Ba Da Hadin Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

135
0

A wani bangare na taimakawa gwamnatin Tarayya shawo kan tarin mastalolin da suka addabi kasar musamman a fannin tsaro, hukumar wayar da kan al’umma ta kasa wato National Orientation Agency ta kaddamar da wani sabon yakin wayar da kan al’umma.

Sabon kamfen din da zai mai da hankali wajen wayar da kan al’umma kan manyan laifuffuka da ke barazana ga zaman lafiyar kasar wadanda suka hada da bangaren siyasa, satar mutane don karbar kudin fansa da shan miyagun kwayoyi da dai sauransu.

Hukumar wayar da kan al’umma a Najeriya ta yi wa taken taron kaddamar da kamfe din kan‘’Samar Da Najeriya Mai Cike Da Tsaro Da Kwanciyar Hankali’’ a wani mataki na dakile tarin matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Dakta Garba Abari, babban shugaban hukumar, ya ce daya daga cikin abin da ke tayar masu da hankali a matsayin ‘yan kasan shi ne tashe-tashen hankali, garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, rushe-rushe na kayan gwamnati da duk abubuwan da suke nuna rashin kyakkyawan tsaro a kasar.

An dai yi Allah wadai kan ire-iren laifufuka da ake aikatawa a kasar musamman ta’ammali da miyagun kwayoyi da ke zama jigon abun da ke kawar hankalin matasa har ya jefa su aikata manya laifuffuka, lamarin da ke dawo da hanun agogo baya ta fuskar tsaro.

Leave a Reply