Home Labarai Tafiye Tafiyen Tinubu: Atiku Ya Bayyana Damuwarsa Matuka

Tafiye Tafiyen Tinubu: Atiku Ya Bayyana Damuwarsa Matuka

11
0
Atiku
Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana damuwa a kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima suka fice daga kasar ba tare da barin wani jagora ba.

A wani tsokaci da ya wallafa a shafinsa na fezbuk, Atiku yace yana ta samun labaran dake nuna cewar shugaban da mataimakin sa sun fice daga Najeriya.

Atiku,  ya ce abin damuwa ne yadda wadannan shugabanni biyu zasu fice lokaci guda a kasar da ke fuskantar kalubale da dama.

Tsohon mataimakin shugaban yace abinda ke damun sa yanzu shine, wanene yake jan akalar kasar a wannan lokaci? Inda ya kara da cewar ko itace ke jagorancin kanta da kanta?

‘Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci a kan bacewar shugaba Bola Ahmed Tinubu kwanaki 7 da suka gabata, bayan halartar taron zuba jari a kasar Saudi Arabia.

Ya zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa daga fadar shugaban a kan inda shugaban ya shiga.

Leave a Reply