Home Home Tabbatar Da Tsaro: An Tura ‘Yan Sanda Dauke Da Makamai Akan Titin...

Tabbatar Da Tsaro: An Tura ‘Yan Sanda Dauke Da Makamai Akan Titin  Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna

79
0

Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya ya ce ya ba da umarnin tura jami’an tsaro ɗauke da makamai domin tabbatar da tsaro a sufurin jirgin ƙasa da ya dawo aiki daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, 5 ga watan Disambar, 2022.

Rundunar ta ce ta tura jami’anta na kwantar da tarzoma masu aiki da karnuka da na ofishin tattara bayanan sirri da sashen kula da ababen fashewa, da ‘yan sandan kula da sufurin jirgin ƙasa domin fara wannan jigila.

Yanzu dai hukumomi sun ce sun tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki domin ci gaba da sufurin jirgin ƙasan na Abuja.

A cikin wata sanarwa da Rundunar ‘yan sanda ta fitar a ranar Lahadi ta ce an tura jami’an nata ne zuwa manyan tasoshin jirgin da cikin tarago-tarago na jiragen da ke bin hanyar Abuja zuwa Kaduna domin tabbatar da tsaron fasinjoji da dukiyarsu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasar NAN ya ambato Hukumar Kula da Sufurin Jirgin ƙasa ta Najeriya na cewa gwamnati ta yi asarar sama da Naira miliyan 113 a tsawon wata takwas da jiragen suka shafe ba sa aiki.

A ƙarshen watan Maris din da ya gabata ne, aka dakatar da sufurin jirgin ƙasan, bayan ‘yan fashin daji sun kai hari tareda sace wasu daga cikin fasinjojin Jirgin.

Leave a Reply