Home Labaru Ta’aziyya: Osinbajo Ya Ziyarci Iyalan Marigayiya Reuben Fasoranti

Ta’aziyya: Osinbajo Ya Ziyarci Iyalan Marigayiya Reuben Fasoranti

331
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci babban Jigon kungiyar Yarbawa ta Afenifere da aka kashe ‘yarsa Pa Reuben Fasoranti.

Osinbajo dai ya je yi wa Reuben Fasoranti ta’aziyya ne game da rashin da ya yi, inda ya sa sunan sa cikin rajistar wadanda su ka je ta’aziyyar Marigayayi Funke Olakunrin.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci babban Jigon kungiyar Yarbawa ta Afenifere da aka kashe ‘yarsa Pa Reuben Fasoranti

Mataimakin shugaban kasar, ya ce ba za su iya bayyana cikakken alhinin su ba, amma za su tsaya wajen jajenta wa iyakan marigayiwar musamman mahaifin ta.

Farfesa Osinbajo, ya kuma gana da mahaifin marigayiyar a cikin dakin sa ba tare da kowa ya shiga tsakanin su ba.

Idan dai ba a manta ba, an harbe Funke ne a kan titi lokacin da ta ke tafiya a daidai Garin Kajola da ke kan hanyar Legas zuwa Garin Benin, lamarin da tuni shugaba Muhammadu ya bukaci a gudanar da bincike a kan lamarin.

Leave a Reply