Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Sanda Sun Kama Rikakkun Masu Safarar Makamai A Jihar Oyo

Ta’addanci: ‘Yan Sanda Sun Kama Rikakkun Masu Safarar Makamai A Jihar Oyo

258
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo, ta sanar da kama wasu ‘yan bindiga hudu, wadanda su ka shahara wajen safarar makamai da alburusai ga kungiyoyin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

An dai kama mutanen ne dauke da alburusai dubu10 kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda na jahar Shina Olukolu ya bayyana, inda ya ce a ranar 23 ga watan Yuli su ka kama mutanen da misalin karfe 2 na dare a unguwar Oke-Bola a garin Ibadan.

kwamishinan ‘yan sanda na jahar Shina Olukolu

Kwamishinan, ya ce ‘yan bindigar sun boye makaman ne a cikin wata mota kirar Toyota Sienna da Toyota Camry, yayin da daya daga cikin su ya ce ba su da lasisin saida harsashi, amma ya na kai wa mafarauta alburusai.
domai.

Leave a Reply