Home Labarai Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Tashi Kauyuka Da Dama A Kaduna

Ta’addanci: Yan Bindiga Sun Tashi Kauyuka Da Dama A Kaduna

115
0
bandit
bandit

Mazauna wasu ƙauyuka 10 a Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu saboda harin ’yan ta’adda masu satar mutane.

Da dama daga cikin mutanen yankin sun tako da ƙafa ne domin samun mafaka a garin Giwa, hedikwatar karamar hukumar.

An ga yara kanana da mata cikin yanayi na firgici suna ta tuttudowa cikin garin Giwa domin tsira da rayukansu.

Wakilin mazaɓar Giwa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Umar Auwal Bijimi, ya ce , an fara gudun hijirar ne tun bayan canza wa wani soja mai ƙwazo kuma kwararre mai suna Sajan Usman Hamisu Bagobiri wurin aiki.

Ya ce Sajan Bagorbiri ya taka muhimmiyar rawa wurin yakar ’yan fashin dake addabar yankin.

Dan majalisar ya ce, rashin Sajan Bagobiri ya bai wa ’yan ta’addar kwarin guiwa, lamarin da ya sa suke ta kai munanan hare-hare a kauyukan.

Bijimi ya ce, kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Gogi da Unguwar Bako da Marge da Tunburku sai  Bataro da Kayawa da kuma Yuna.

Leave a Reply