Home Labaru Ilimi Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibin Shekarar Karshe A Jami’ar Danfodio

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibin Shekarar Karshe A Jami’ar Danfodio

489
0

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani dalibin da ke shekarar sa ta karshe mai suna Aliyu Maidamma a jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, yayin da ya rage saura ‘yan kwanaki kalilan a fara jarrabawar karshen kammala rabin zagayen zango.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun sace Aliyu ne a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da ya ke kan hanyar sa ta komawa Sokoto bayan kammala hutun karamar Sallah.

Dan’uwan dalibin da aka sace Ibrahim Sanni Maidamma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a magana ta karshe da su ka yi da Aliyu ya ya shaida ma shi cewa ya na kan hanyar sa ta komawa makaranta.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kungiyar daliban jami’ar’ Kwamred Faruk Barde, ya ce kungiyar daliban ba ta gana da iyayen Aliyu domin samun karin bayani ba.

Leave a Reply