Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansar Daliban Da Su Ka Sace...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansar Daliban Da Su Ka Sace A Kaduna

300
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce ta na kan tattaunawa da ‘yan bindigar da su ka sace dalibai mata 6 da malaman su 2 daga kwalejin Engravers da ke karamar hukumar Chikun.

Yayin Karin bayani a kan halin da ake ciki, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i, yace an soma tattaunawar ne, bayan ‘yan bindigar sun bukaci a biya su kudin fansa kafin sakin daliban da kuma malaman su.

Duk da cewa Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin tsaro a wasu yankuna, sace daliban da ‘yan bindigar su ka yi ya zama bakon abu.

Tun bayan sace daliban dai, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta kaddamar da farautar ‘yan bindigar kamar yadda kakakin ta Yakubu Sabo ya tabbatar.