Home Labarai Ta’Addanci: ’Yan Bindiga Sun Kashe Hakimin Da Suka Sace A Bauchi

Ta’Addanci: ’Yan Bindiga Sun Kashe Hakimin Da Suka Sace A Bauchi

62
0


’Yan bindiga sun kashe Hakimin Kauyen Riruwai da ke
Gundumar Lame a masarautar Bauchi a Karamar
Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi.


Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko wasu ‘yan bindiga ne da suka kai hari tare da yin garkuwa da shi a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, 2024.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ‘yan bindigar sun shiga fadar marigayin kai tsaye, inda suka yi awon gaba da shi.


Majiyar ta ce marigayin ya shafe kwana daya a hannun ’yan bindigar kafin daga bisani suka kashe shi tare da jefar da
gawarsa a kan hanyar kauyen.


Daya daga cikin masu sarautar gargajiya na kauyen ya tabbatar da faruwar lamarin.


Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ta ci tura domin bai amsa kiran da aka masa ba.

Leave a Reply