Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hare-Hare A Karamar Hukumar Igabi A Kaduna

‘Yan bindiga sama da 100 ne suka kai hari a garuruwan Kerawa, Rago, Zariyawa da Marina dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 3 suka kuma jikkata mutane 6, sannan suka sace dabbobi da kayan abinci.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar kan babura, dauke da manyan makamai suka afkawa garuruwan.

Hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari, da Igabi, da Giwa

Hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Birnin Gwari, da Igabi, da Giwa ya kara janyo fargaba ga manoma a daminar bana.

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta na daukar matakan sirri wajen magance matsalar tsaro a wadannan yankuna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan, ya ce bayan samun labarin abinda ya faru, aka tura jami’an tsaro wadannan yankunan, kuma sojojin kasa sun fattaki ‘yan bindigar, sannan na sama suka kai musu farmaki ta sama.

Ya kara da cewa a yanzu haka gwamnati da jami’an tsaro sun dauki matakin tsaro a wadannan yankunan.

Da ma dai jihar Kaduna na cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan-bindiga da kuma sace-sacen mutane don neman kudin fansa.

Exit mobile version