Home Labarai Ta’Addanci: Majalisa Ta Ba Da Wa’Adin Nemo Ɓata-Garin Da Suka Kashe Sojoji A...

Ta’Addanci: Majalisa Ta Ba Da Wa’Adin Nemo Ɓata-Garin Da Suka Kashe Sojoji A Delta

57
0

Majalisar Wakilai ta bayar da wa’adin mako hudu na
tabbatar da an nemo wadanda suka kashe sojojin Najeriya
17 a Jihar Delta.


An yi wannan kira ne bayan wani dan majalisar, Babajimi Benson daga Jihar Legas ya gabatar da kudirin gaggauta nemo bata-garin da suka kashe sojojin a ranar Alhamis.\


Majalisar wadda ta bayyana takaici, ta bai wa rundunar sojin kasar umarnin nemo wadanda suka aikata wannan mummunan al’amari ga dakarun da ke bakin aiki.

Babajimi Benson ya ce, “abin akwai ta da hankali kwarai sosai yadda ɓata-garin suka hallaka sojojin.


Ya kara da ceea Sojojin nan da aka kashe fa sasanci za su yi tsakanin jama’ar Okoloba da na Bomadi  na Jihar Delta, amma aka kasashesu. Sannan bayan an kashesu kuma aka farke kirjinsu aka ciri zukatansu da wasu sassan jikinsu. Dole ne a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.


Binciken mu ya gano cewa shugaban wannan runduna da aka hallaka gwarzon soja ne, domin kuwa yana daya daga cikin wadanda suka karbo wasu yankuna da ’yan kungiyar Boko Haram ta yi iko da su a shekarun baya.

Leave a Reply