Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta’addanci: Kungiyar Boko Haram Ta Mamaye Wasu Garuruwa a Jihar Neja

Rahotanni daga Jihar Neja sunce ƙungiyar Boko Haram ta mamaye garuruwa da dama na jihar, inda suke bai wa mazauna ƙauyuka kuɗi tare da sanya su cikin mayakansu.

Wasu mazauna yankin sun ce mayaƙan sun mamaye wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro suna yi wa mutane wa’azi, Al’amarin da ya jefa jama’ar yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Wani mazauni yankin ya shaida wa BBC cewa “Ƴan Boko Haram suna tara mutane suna yi musu wa’azi, suna kuma raba kuɗi a garin Kurebe da Kwaki.

Wannan na zuwa, watanni shida bayan Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar Boko Haram ta kafa tuta a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar a watan Afrilu, ya ce mayaƙan sun kafa tuta ne a ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro.

Wasu rahotanni sunce shugaban ƙaramar hukumar Shiroro da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja Alhaji Sani Idris sun tabbatar da ɓullar mayakan na Boko Haram a wasu yankunan na Neja.

Exit mobile version