Home Labaru Kiwon Lafiya Ta’addanci: Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Bindiga A Rabah Ta...

Ta’addanci: Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Bindiga A Rabah Ta Jihar Sokoto

306
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Hare-Haren Da Wasu ‘Yan Bindiga Suka Kai A Wasu Kauyuka Da Ke Karamar Hukumar Rabah A Jihar Sokoto.

Mai Magana Da Yawun Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu Ya Bayyana Haka A Abuja,Inda Ya Tabbatar Da Cewa, An Sanar Da Shugaban Kasa Buhari A Kan Halin Da Ake Ciki A Jihar, Kuma Tuni ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Hannu A Kai Hare-Haren.

Shugaba Buhari Ya Kuma Mika Ta’aziyyar Sa Ga Gwamnan Jihar Aminu Tambuwal Da Sauran Al’ummar Jihar Bisa Wannan Mummuna Hari Da ‘Yan Bindigan Suka Kai Akan Wadanda Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba, Tare Da Bada Tabbacin Hukunta Wadanda Aka Samu Da Hannu A Aika-Aikar.

A Karshe Buhari Ya Yiwa Wadanda Suka Samu Rauni Addu’ar Samun Lafiya Cikin Gaggawa, Sannan Ya Ce Gwamnatin Sa Ba Za Ta Yi Kasa A Guiwa Ba Wajen Yaki Da Ayyukan Ta’addanci A Nijeriya.