Home Labaru Ta’addanci: Boko Haram Ta Yi Yunkurin Kai Hari A Garin Damaturu Na...

Ta’addanci: Boko Haram Ta Yi Yunkurin Kai Hari A Garin Damaturu Na Jihar Yobe

1311
0

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun yi yunkurin kai hari a garin Damaturu na jihar yobe, amma rundunar sojin Nijeriya ta yi nasarar dakile shi.

Wasu mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa, sun ji karar shawagin jiragen yakin sojoji da kuma karar manyan bidigogi ana ta harbe-harbe.

Al’ummomin garin, sun kuma roki gwamnati ta rika daukar matakai a kan miyagun mutanen kafin su kai hari a garuruwan su.

Wata majiya mai tushe daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatar wa manema labarai cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun yi yunkurin kai hari, amma rundunar sojin ta dakile shi.

Wani masanin tsaro, ya ce a jihar Yobe ne ta’addancin Boko Haram ya fara kafin ya bazu zuwa jihar Borno da kuma sauran garuruwa.