Home Labaru Ta’addanci: Boko Haram Ta Kashe Mutane 13 A Chadi

Ta’addanci: Boko Haram Ta Kashe Mutane 13 A Chadi

694
0

A gabashin Chadi mutane 13 aka sanar da mutuwar su bayan da mayakan Boko haram suka kai wani kazamin hari a kauyen Cellia dake da nisan kilometa 40 da birnin Bol.

Harin da aka kai da safiyar Alhamis, mayakan na Boko Haram sun kashe wani mai gari tare da cinnawa gidaje da dama huta.

Biyu daga cikin mutanen da aka kashen, an yi musu yankar rago ne.

Akalla mutane dubu 27 ne aka rasa tun daga shekara ta 2009 lokacin da kungiyar ta Boko Haram ta samu shiga kasar ta Chadi. Bayan harin dai rundunar sojin kasar  ta sanar da tura dakarun sojin zuwa yankin.