Home Labaru Ta’addanci: Allah Kadai Zai Iya Kare Iyakokin Nijeriya Ba ‘Yan Sanda Ba...

Ta’addanci: Allah Kadai Zai Iya Kare Iyakokin Nijeriya Ba ‘Yan Sanda Ba – Shugabannin Tsaro

333
0

Biyo bayan ganawar su da shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja, shugabannin hukumomin tsaro sun ce Allah kadai ne mai iya tsare iyakokin Nijeriya.

A karshen ganawar, shuwagabannin tsaron sun bayyana rashin tsaro a kan iyakokin Nijeriya a matsayin ummul-haba’isin yawaitar ayyukan ta’addanci a Nijeriya.

Shugabannin tsaron da su ka halarci ganawar dai sun hada da shugaban ma’aikatan tsaro Janar Gabriel Olonisakin, da shugaban dakarun sojin kasa Janar Tukur Buratai, da shugaban sojin ruwa Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas, da na rundunar sojin sama Air Marshall Abubakar Sadique.

Sauran sun hada da, mai ba kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno, da Ministan tsaro Mansur Dan Ali, da shugaban hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Abubakar, shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, da Yusuf Magaji Bichi na hukumar tsaro ta farin kaya.

Leave a Reply