Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta Kacame Tsakanin Gwamnati Da Kamfanonin Raba Wutar Lantarki

Alamomin tabarbarewar wutar lantarki sun kunno kai a Nijeriya, yayin da kamfanonin saida wuta wato GENCOs su ka yi wa gwamnatin tarayya barazanar janyewa daga saye da sayar da wutar Lantarki.

Hakan kuwa, ya biyo bayan wasu makudan kudade naira biliyan 2 da miliyan 700 da aka nemi kowanen su ya biya.

An ce kudaden da ake so su biya, harajin kudaden Gas ne da  na kamfani shiga tsakanin harkar kudade tsakanin gwamnati da kamfanonin saida wutar lantarki, NBET.

Matsalar da ta shiga tsakani ce ta sa har gwamnatin tarayya ta nemi zuba naira biliyan 600 domin tallafa wa kamfanonin GENCOs su samu sa’idar harkar lantarki a fadin Nijeriya.

Sai dai kamfanonin sun bayyana cewa, ba za su amince da harajin naira biliyan 2 da miliyan 700 da aka kakaba masu da rana tsaka ba.

Babbar Sakatariyar Kungiyar Kamfanonin Raba Wutar Lantarki Joy Ogaji, ta ce tun ranar 13 Ga Satumba, kamfanin NBET ya bada umarnin biyan kudaden ko kuma su fuskanci matsalar rashin wadatar da su da Iskar Gas.

Exit mobile version