Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sulhu: Isra’ila Ta Janyewa Falasdinawa Dokar Hana Kamun Kifi

Kasar Isra’ila ta janye dokar haramcin kamun kifi da ta kakabawa, kananan jiragen ruwan Falasdinawa da ke sana’ar su a gabar ruwan da ke kan iyakarta da yankin Gaza.

Matakin dage haramcin kamun kifin, wani bangare ne na soma aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin suka cimma, bayan da a makon da ya gabata, Jiragen yakin Isra’ila suka kai wa cibiyoyin mayakan da ke gaza farmaki, a matsayin martini kan harba makaman roka akalla 250 da suka yi cikin Isra’ilar. A baya dai sojin ruwan Isra’ila kan bude wuta kan Falasdinawan da ke sana’ar ta ta kamun kifi a duk lokacin da suka ketara kan iyakar ruwan da ke tsakaninsu.

Exit mobile version