Ministan sufuri Mu’azu Sambo ya ce za a yi ƙarin kuɗin tikitin jirgin ƙasan Abuja, zuwa Kaduna.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da manema labaru, a wurin gwajin jirgin a shirye-shiryen da ake yi na dawo da sufurin.
Ya ce za a yi ƙarin ne bisa dogaro da sauyin da aka samu na tattalin arziƙi.
Ministan ya ce ma’aikatar sufuri na tattaunawa da hukumar lura da jiragen ƙasa ta kasa domin ganin ko za a yi ƙarin farashin ne nan take ko kuma za a jinkirta.
Ya ce “kowa ya san cewa farashi ya tashi, hatta farashin tikitin jiragen sama ya tashi, wanda hakan ne yasa ake duba yuwuawar ƙara farashin tikitin jirgin ƙasan”
You must log in to post a comment.