Gwamnatin Tarayya, ta bada umurnin karin jiragen kasa biyu da za su rika jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna domin rage matsalar cunkoso.
Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bada umurnin, yayin da ya ke ziyarar gani da ido na wata-wata a kan ayyukan hanyar jirgin kasa da ta tashi daga Lagos zuwa Ibadan.
Wata majiya ta ce akwai matsalar yawan fasinjoji a tashar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna saboda ayyukan masu garkuwa da mutane da ke gudana a hanyar.
Ameachi ya ce hukumar kula da tashoshin jiragen kasa ta Nijerya za ta kai karin jiragen kasa biyu daga Itakpe zuwa Warri da kuma hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya na mai cewa za a hukunta duk jami’in da aka samu yana saida tikiti ba bisa ka’ida ba.
You must log in to post a comment.