Home Labaru Sudan: Masu Zanga-Zanga Sun Yanke Hulda Da Gwamnati

Sudan: Masu Zanga-Zanga Sun Yanke Hulda Da Gwamnati

239
0

Shugabannin masu zanga-zanga a Sudan sun ce ba su ba gwamnatin soja ta kasar wadda ta maye gurbin hambararren shugaba Omar al-Bashir.

Suna zargin gwamnatin tana dauke da sauran mambobin tsohuwar gwamnatin al-Bashir.

Dubban masu zanga-zangar sun mamaye harabar ma’aikatar tsaro ta kasar a birnin Khartoum domin tataunawa gabanin sanarwar wata sabuwar gwamnati ta farar hula da suke o ta karbi ragamar mulki daga hannun gwamnatin sojin kasar.

A nata bangaren kuwa, gwamnatin sojin ta ce a shirye take ta mika mulki, amma ta fi so a yi hadin gambiza, wato a kafa gwamnatin sojoji da fararen hula. Amma kakakin masu zanga-zangar Mohamed al-Amin ya ce sun dawo daga rakiyar majalisar sojojin da ke mulkin kasar, kuma suna kallonta a matsayin “wani bangare na tsohuwar gwamnatin” kuma su sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya har sai sun cimma bukatunsu.