Home Labaru Steven Gerrard Ya Zama Kocin Aston Villa

Steven Gerrard Ya Zama Kocin Aston Villa

129
0

Aston Villa ta naɗa Steven Gerrard a matsayin sabon kocin ta kan kwantiragin shekara uku da rabi.

Gerrard ya maye gurbin Dean Smith, inda ya bar aikin sa na horar da ƙungiyar Rangers ta Scotland.

Tsohon kyaftin ɗin Liverpool mai shekara 41 ya bar Rangers ne bayan ya jagorance ta lashe babbar gasar Scotland.

Yanzu haka Villa tana mataki na 16 a teburin Premier League da maki biyu tsakanin ta da ‘yan ukun ƙarshe.

Steven Gerrard yace aston Villa ƙungiya ce mai ɗumbin tarihi da al’adu a ƙallon Ingila kuma yana alfaharin zama kocin ta.

Leave a Reply