Home Labaru Sri Lanka: Akalla Mutum 300 Suka Mutu A Hare-Hare

Sri Lanka: Akalla Mutum 300 Suka Mutu A Hare-Hare

336
0

Kusan mutum 300 ne aka tabbatar da mutuwarsu a jerin hare-haren da aka kai a Sri Lanka, yayin da kusan 500 suka jikkata.

Wakilin kafar yada labarai ta BBC dake lardin Colombo ya cewa an kara samun wani harin bam a wani otel dake a kusa da wani gidan adana namun daji, inda wasu ‘yan sanda biyu suka rasa ransu.

Sai kuma wani sabon hari da aka kai a lardin Dematagoda wanda zuwa hada wannan labarin babu cikakken bayani a kai

Wadannan su ne hare-hare na 8 da aka kai a ranar Lahadi a coci-coci da kuma Otel-Otel a Sri Lanka, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300.

Daga cikin wadanda aka kashe dai akwai ‘yan kasashen waje 35, da kuma harin ya jikkata mutum sama da 450.

An dai sami rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci guda uku a Kochchikade da Negombo da kuma Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Easter.

An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Colombo.Sai kuma a yanzu aka kara samun wadannan da ya zama na bakwai na otel din da ke lardin Colombo da kuma na takwas da aka kai a lardin Dematagoda.A yanzu haka dai gwamnatin kasar ta saka dokar hana fita sakamakon lamarin da ke kara ta’azzara.

Leave a Reply