Home Labarai Soyinka Ya Yi Allah Wadai Da Kalaman Baba Ahmed

Soyinka Ya Yi Allah Wadai Da Kalaman Baba Ahmed

5
0

Fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya yi Allah wadai
da kalaman dan takarar mataimakin shugaban kasa na
Jam’iyyar Labour Datti Baba Ahmed.

Soyinka ya bayyana irin kalaman da Baba Ahmed ke yi a matsayin karan-tsaye ga bangaren shari’a da tafarkin dimokradiyyar Nijeriya baki daya.

Wannan dai ya biyo bayan kalaman Datti Baba-Ahmed yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya bukaci shugaba Buhari da shugaban alkalan Nijeriya kada su kuskura su rantsar da Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Datti Baba Ahmed, ya ce bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi da kuma gabatar masa da takardar shaida da hukumar zabe ta yi ya saba wa dokar Nijeriya.

Farfesa Soyinka, ya gargadi kafofin yada labarun Nijeriya a kan irin rahotanni da hirarrakin da su ke yi, wadanda ka iya tada hankali ko kuma gabatar da rahotannin da ba haka su ke ba, wadanda ya ce za su iya tada hankalin jama’a ko haddasa tarzoma.

Ya ce sau uku ya na aike wa Peter Obi sakonni, inda ya ke shaida ma shi cewa muddin ya fadi zabe ya zargi magoya