Fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya yi Allah-Wadai da tsare jagoran masu fafutukar kare hakkin dan Adam da ya nemi jama’a su nuna rashin amincewa da sha’anin gwamnatin Nijeriya.
Sowore, wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a zaben shekara ta 2019 a karkashin jam’iyyar AAC, ya shiga hannun jami’an tsaro na farin kaya, biyo bayan kiran da ya yi na neman jama’a su nuna rashin amincewa da yadda al’amura su ka tabarbare a Nijeriya.
Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Sowore ya yi shelar jama’a su fito domin juyin juya-hali da nufin neman kawo sauyi a kan yadda gwamnati ta bari talauci da rashin tsaro da kuncin rayuwa su ka yi wa Nijeriya dabaibayi.
Farfesa
Soyinka, ya misalta lamarin da rashin adalci da kuma dakile ‘yancin dan Adam da
kundin tsarin mulkin kasa ya tanada, inda ya ce har yanzu Nijeriya na ci-gaba
da amfani ne da kundin tsarin mulki da ya samo asali daga sojoji.