Home Labaru Soke Tallafi: Angola Ta Kara Farashin Mai Amma Banda Masu Motoci Da...

Soke Tallafi: Angola Ta Kara Farashin Mai Amma Banda Masu Motoci Da Baburan Haya

153
0

Gwamnatin Angola ta ce ba matsin lamba daga asusun bayar da tallafi na duniya, IMF ba ne ya sa ta soke tallafin mai a kasar.

A jiya Alhamis ne ministar kudin kasar Vera Daves ta ce matakin ya biyo bayan nazarin da gwamnatin kasar mai cin gashin-kanta ta yi ne a kai.

Batun ya taso ne bayan da gwamnati ta kara farashin man daga kudin kasar kwanza 160 zuwa kwanza 300 a kan lita daya, wanda yake kwatankwacin dala $0.27 zuwa $0.51.

Sai dai karin farashin bai shafi motoci da baburan haya ba, inda ake ba wa masu sana’ar sufurin wani kati na musamman na sayen man da shi.

Kasar ta Angola wadda ke yankin kudancin nahiyar Afirka, ita ce kan gaba a yanzu wajen yawan man da ake fitarwa kasuwar duniya daga nahiyar duk da cewa ba ta kai Najeriya yawan arzikin man ba.

Leave a Reply