Home Home Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanin IPOB Tare Da Kwato Makamai

Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanin IPOB Tare Da Kwato Makamai

91
0

Rundunar sojin Nijeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya, sun lalata sansanin ‘yan nungiyar awaren Biafra ta IPOB da takwarar ta ta ESN a birnin Asaba na jihar Delta.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce jami’an ta sun kaddamar da samame a kan sansanin ‘yan awaren da ke tsakiyar dajin Asaba, inda su ka samu nasarar kwato makamai.

Sojojin dai sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a lokacin samamen, inda daga bi-sani ‘yan bindigar su ka gudu daga maɓoyar su.

Sanarwar ta ce, sojojin sun kama daya daga cikin mayaƙan ‘yan awaren, tare da ƙwato bindigogi biyar kirar AK-47, da manyan bindigogi masu sarrafa kan su guda uku da wata ƙirar G3 da ƙamar bindiga guda.

Sauran abubuwan da dakarun sojin suka ƙwato, sun hada da kwanson zuba alburusai biyar, da gatari da kuma tutar kungiyar IPOB.

Leave a Reply