Home Home Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda 6 Da Kwato Makamai Da...

Sojoji Sun Yi Nasarar Kashe ‘Yan Ta’adda 6 Da Kwato Makamai Da Dama A Kaduna

44
0

Dakarun ‘Operation Forest Sanity’, tare da hadin gwiwar helkwatar tsaro sun kashe ‘yan ta’adda shida, tare da kwato makamai da alburusai a wani samame da su ka kai a boye.

A wata sanarwa da daraktan hulda da manema labarai na rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ya fitar, ya ce sojojin sun kai farmakin ne a asirce a kauyukan Maidaro da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Ya ce a wani artabu da su ka yi da ‘yan ta’addan, sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 6, tare da kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyar, da harsasai na musamman 192 da babura uku da sauran abubuwa daban-daban.

Babban hafsan sojin, ya yaba wa sojojin tare da yin kira ga jama’a su ba sojoji bayanai masu inganci kuma a kan lokaci kan ‘yan ta’adda da duk wasu masu ayyukan ta’addanci a yankin su.

Leave a Reply