Home Labaru Sojoji Sun Kwace Makaman Mayaƙan Iswap Da Boko Haram A Jihar Borno

Sojoji Sun Kwace Makaman Mayaƙan Iswap Da Boko Haram A Jihar Borno

240
0

Rundunar sojin Najeriya ta kashe mayaƙan Boko Haram da na ISWAP yayin wani harin da ta kai musu a ranar Laraba.

Jami’in watsa labarai na sojojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne sanar da hakan a yau Alhamis.

Acewarsa Sojojin sun yi wa mayaƙan kwanton ɓauna ne a kan hanyar Kwadal zuwa Amuda bayan sun samu labarin hare-haren da mayaƙan ke kaiwa a yankunan, inda hakan ya sa sojojin suka jira su a wata maraba inda suka buɗe musu wuta.

Sojojin dai sun samu nasarar ƙwace bindiga samfarin machine gun da gurneti uku da kuma harsasai 62 da babur ɗaya da kekuna uku.

Ko a kwanakin baya sai da mayaƙan ISWAP ɗin suka kashe wani janar ɗin soji da wasu sojoji uku a jihar Borno

Leave a Reply