Home Coronavirus Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 17 A Kaduna

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 17 A Kaduna

512
0
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 17 A Kaduna
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 17 A Kaduna

Hedkwatan tsaron Nijeriya ta ce dakarun rundunar sojojin Nijeriya na Operations Thunder Strike da hadin gwiwan rundunar Operation GAMA AIKI sun kashe yan bindiga 17 a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Mai magana da yawun hedkwatanr Manjo Janar John Enenche ya bayyan hakan a Abuja, tare da cewa wasu ‘yan bindiga da dama sun tsere da raunukan a jikin su.

Harin dai, an kai shine bisa zargin cewa ‘yan bindigan su na  boye a mabuyar su da ke kusa da kauyukan Mashigi da Galbi da Damba da Kabarasha a yankin Gwagwada.

Enenche ya kara da cewa, harin na cikin kokarin da rundunar sojojin Nijeriya na fatattakar ‘yan bindiga da sauran bata gari a jihar Kaduna.

Sai dai a lokacin ar’tabaun, an lalata wasu gidaje uku da coci daya a kauyen Kabarasha, amma babu wani farar hula da ya rasa ran sa, sannan  Enenche ya bayyana rashin jin dadin sa game da afkuwar lamarin, inda ya kara da cewa an kafa kwamitin bincike tare da hadin gwiwar gwamnatin Kaduna.

Rundunar sojojin ta kuma ba ‘ yan Nijeriya tabbacin cigaba da aiki tukuru domin ganin zaman lafiya da tsaro ya dawo yankin Arewa maso yammacin nijeriya dama kasa baki daya.