Rundunar Operation Hadin Kai ta sojin Nijeriya da ke yaki da Boko Haram, ta gudanar da gasar karatun Al-Kur’ani ta matasa a yankin Monguna na Jihar Borno.
Muhammad-Nur Mustapha da ya zama gwarzon gasar, ya samu karramawa da kyautar kujerar zuwa aikin Umrah.
Wanda ya zo na biyu Zaharadeen Yusuf kuma ya samu kyautar kuɗi Naira dubu 300, sai Mohammed Ali da ya zo na uku kuma ya samu kyautar Naira dubu 200.
Babban Limamin Monguno Alhaji Liman Kaumi, ya jagoranci malamai wajen halartar Musabaqar Al-Ƙur’ani da sojojin su ka shirya, yayin da Ajiyan Monguno Alhaji Zanna Bulama ya jagorinci sarakuna zuwa wajen taron.
Da ya ke jawabi yayin buɗe musabakar, mai masaukin baki kuma Kwamandan Runduna ta 111 Manjo-Janar A.E Abubakar, ya ce gasar za ta taimaka wajen samun nasara a yaki da ta’addanci ba tare da amfani da ƙarfin soji ba.