Home Labaru Sojoji Sun Bukaci Gwamnoni Su Daina Katsalandan Wajen Yaki Da ‘Yan Ta’Adda

Sojoji Sun Bukaci Gwamnoni Su Daina Katsalandan Wajen Yaki Da ‘Yan Ta’Adda

188
0

Sabon Shugaban rundunar sojin kasa ta Nijeriya Manjo Janar
Taoreed Lagbaja, ya bukaci gwamnoni su ba su damar kawar
da ‘yan ta’addan da su ka hana zaman lafiya a sassan Nijeriya
ba tare da katsalandan ba.

Yayin da ya ke ganawa da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, Lagbaja ya yi watsi da duk wani yunkuri na tattaunawa da ‘yan ta’adda kamar yadda wasu jama’a ke bukata, inda ya ce sun gaji da yaudarar da ‘yan ta’addan ke yi domin samun lokacin sake tara makaman kai sabbin hare- hare.

Ya ce ‘yan ta’addan sun ki bada kai bori ya hau, saboda yadda su ke amfani da tattaunawar da ake yi da su wajen sake tara makamai, don haka babu wani dalilin sake hawa teburin sulhu da su.

Janar Lagbaja ya bukaci irin wadannan ‘yan ta’addan su gaggauta kwashe kayan su su bar Najeriya, ya na mai gargadin cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin bayan su.

Leave a Reply