Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Manjo Janar Taoreed
Lagbaja, ya kaddamar da sabuwar rundunar ya ki da
ta’addanci a karamar hukukumar Mangu ta jihar, domin kawo
karshen hare-hare da kisan jama’a babu gaira babu dalili a
Mangu da wasu sassan jihar baki daya.
Rundunar Sojin Nijeriya dai ta kaddamar da rundunar musamman da aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4.
Rikicin baya-bayan nan a yankin dai ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 300 a karamar hukumar Mangu da kewaye a cikin watanni biyu, sakamakon hare-hare mabanbanta da ‘yan bindiga su ka kai.
Bayan kaddamar da sabuwar rundunar, shugaban sojin kasa na Nijeriyar ya kuma yi wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a wata makarantar firamare da ke garin.