Home Home Sojin Najeriya Sun Kashe Barayin Daji 128 Da ‘Ƴan Boko Haram 140

Sojin Najeriya Sun Kashe Barayin Daji 128 Da ‘Ƴan Boko Haram 140

90
0

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ɓarayin daji 128 a arewa maso yammaci da kuma ‘ƴan Boko Haram 140 a arewa maso gabashin ƙasar nan.


Rundunar sojin ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai
magana da yawunta Bernard Onyeuko ya fitar inda ya bayyana
irin nasarorin da ayyukan rundunonin sojin suka samu a sassan
Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.


Rundunar ta ce alƙalumman sun shafi ayyukan rundunoninta na
tsawon mako biyu daga ranar 11 ga Nuwamba zuwa 25 ga wata.
Sanarwar ta ce an yi wa sansanonin ƴan bindiga da ƴan Boko
Haram ruwan wuta da kama wasu daga cikinsu.


Sai dai rundunar sojin ba ta bayyana yawan jami’anta da aka
kashe ba a yankunan da ke fama da matsalar tsaro ba.


Wannnan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ba
manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan umarnin fatattakar ƴan
bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda ƙaruwar
yawaitar hare-hare a sassan ƙasar nan.