Home Labaru Kiwon Lafiya Soja Ya Fusata Ya Karya Wa Ma’Aikaciyar Jinya Ƙafa A Jihar Kwara

Soja Ya Fusata Ya Karya Wa Ma’Aikaciyar Jinya Ƙafa A Jihar Kwara

16
0

Wani jami’in soji ya karya ma wata ma’aikaciyar jinya kafa sakamakon duka birnin Ilorin na jihar Kwara.

Lamarin dai ya faru ne, a lokacin da sojan ya kai matar sa mai juna biyu domin ta haihu.

Majiyoyi sun ce, rikicin ya samo asali ne yayin da ma’aikaciyar jinyar ta bukaci a say i kayan haihuwa kafin a karbi matar a ba ta gado a dakin haihuwa.

Sai dai sojan ya buga kai ga kasa cewa gwamnatin jihar ta tanadi irin wadannan kayayakin ta kafe cewa sai ya kai kayan haihuwar, domin a yi amfani da su wajen taimaka wa matar sa haihuwa, lamarin da ya tunzura jami’in sojin har ta kai ga ya karya mata kafa guda.

Kakakin Birgade ta 22 na Rundunar Sojin Nijeriya ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tuni rundunar ta tsare sojan domin ta yi ma shi tambayoyi game da lamarin.