Home Labaru Siyasar Zamfara: Yari Ya Yi Gaugawan Neman Gafarar Allah – Marafa

Siyasar Zamfara: Yari Ya Yi Gaugawan Neman Gafarar Allah – Marafa

1252
0
Sanata Kabiru Marafa
Sanata Kabiru Marafa

Sanata Kabiru Marafa, ya ce Gwamna Abdulaziz Yari ya yi sabon Allah, sakamakon cewa jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda-gwani a jihar Zamfara.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, Marafa ya ce Yari ne ya haddasa duk rikicin da ya yi sanadiyyar hukumar zabe ta hana APC shiga zabe a jihar Zamfara.

Sanatan, ya kuma jinjina wa Kotun Daukaka Kara saboda abin da ya kira hukuncin adalci da ta yanke a kan rikicin siyasar jihar Zamfara.

Marafa ya ce abin takaici ne, a ce shugaba kamar Yari na jihar da ake ikirarin shari’ar Musulunci ya fito ya kantara wa duniya karya.

Ya ce irin wannan shugaba addu’ar neman gafara a wajen Allah ya kamata a nema masa don kada ya hadu da fushin Allah.